‘Yan wasan Liverpool a yunwace suke a karawar da za su yi da Man City- Salah

Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City a a gobe Lahadi a gasar cin kofin Premier yayin da Jurgen Klopp da Pep Guardiola za su yi karawarsu ta karshe a gasar.

Duk da cewa Guardiola ya lashe kambun gasar Premier biyar a cikin shida na baya bayan nan, sai dai Klopp ya kasance yana bashi ciwon kai.

Salah ya ce ba wai Yana kushe yan wasan da suka gabata ba nea kungiyar domin sun taka rawar gani sosai kuma iya iyawarsu.

Inda ya kara da cewa  “A wannan shekara zan ce tawagarmu ta daban ce, saboda ‘yan wasan suna jin yunwa sosai. Muna da kyakkyawar dama ta lashe komai, kawai muna buƙatar yin kokari yadda ya kamata. Ba mu da wani wani uziri na yin rashin nasara.

Kungiyoyin biyu sun hadu sau 15 a gasar Premier tun bayan shekarar 2016, inda Klopp ya samu nasara hudu, yayin da Guardiola ya yi nasara sau biyar.

Doke Liverpool a Anfield a gaban dandazon magoya na daya daga cikin wasan da ya ke ba Guardiola wahala a matsayin kocin City.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories