NPFL 24: Maikaba ya yi kira da a binciki alkalan wasan da suka nuna son zuciya a karawar Pillars da Rivers United

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Abdul Maikaba ya bayyana rashin jin dadinsa da alkalan wasa da suka jagoranci wasan da kungiyarsa ta buga da Rivers United a wasan mako 24

Kungiyar Pride of Rivers ta yi canjarasa da Kano Pillars inda aka ta shi wasa 1-1 a filin wasa na Adokiye Amiesimaka da ke Fatakwal.

Maikaba ya koka da yadda alkalan wasa suka nuna son zuciya, yayin da ya yi kira ga hukumar da ta binciki wasan.

“Idan har hukumar gasar za ta samu lokaci, ta kalli bidiyon wannan wasa tun daga farko har karshe, za su san abin da ya faru, ya kamata ace mun samu maki uku amma a karshe maki daya ne muka samu”

A cewarsa akwai ingantattun qungiyoyin da suke da kyau a Najeriya, kuma suna iya bakin kokarinsu don wakiltar kasar amma idan irin wannan alkalancin za a dinga samu a Najeriya, ba na jin Najeriya za ta samu wakilan da suka cancanta a nahiyar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories