Ku Maida Hatsin Da Kuka Kama Ga Masu Shi -Umarnin Tinubu Ga Kwastam

Shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumar kwastam ta Najeriya da ta mayar da duk wani hatsin da ta kama ga masu shi domin a fitar da su kasuwanni.

 Babban Kwanturolan Hukumar Kwastam (CGC), Bashir Adewale Adeniyi Shi ne ya bayyana hakan a yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a garin Kwangwalam da ke kan iyaka a ƙaramar hukumar Maiadua ta Jihar Katsina a jiya Asabar.

Kwanturolan ya bayyana cewa umurnin da shugaba Tinubu ya bayar hakan na nufin cewar ƴan Najeriya za su sami arhan abinci.

Sannan kuma ya ƙara da cewa duk wanda za a mayar masa da kayan hatsin sa sai ya yarda a gida Najeriya kaɗai zai sayar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories