Azumi:Wani Malami Ya Buƙaci Musulmai Da Su Nisanci Kafofin Soshiyal Mediya

Wani malami mai suna Dr Nafiu Ahmed Arikewuyo Al-Jawharih, ya buƙaci al’ummar Musulmi da su nisanci shafukan sada zumunta a watan Ramadan.

 Malamain ya ce yin hakan zai sa, musulmai su nisanci ayyukan da basu dace ba

Al-Jawharih ya yi wannan jawabin ne a wajen wani taron karawa juna sani na watan Ramadan da kungiyar Muslim Congress (TMC) reshen jihar Kwara, tare da sauran ƙungiyoyin addinin musulunci suka shirya.

 Ya ƙara da cewae “Ya kamata Musulmai a wannan watan su nisanci kafar Facebook da ma sauran shafukan sada zumunta saboda tsarkakuwa daga kallon abinda bai kamata ba.Duba da yadda irin waɗannan kallace kallace ke da illa ga azumi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories