Ƴan Bindiga Sun Sako Sauran Ɗaliban Jami’ar Gusau Da Su Ka Sace

A yau ne rahotanni suka bayyana cewar Ƴan bindiga sun sako sauran ɗaliban jami’ar Gusau da ke tsare a hannun su .

A zantawa da BBC ta yi da wata ƴar uwar ɗaya daga cikin waɗanda aka sace ta bayyana cewa a jiya Asabar ne suka sami kira daga ƴar uwar su cewa an yi nasarar karɓo su hannun ƴan bindigar daga dajin Birnin Gwari suna Abuja .

In ba a Manta ba a watannin baya ne dai ƴan bindiga su ka dira ɗakunan kwanan ɗalibai mata na jami’ar inda suka yi awon gaba da ɗalibai da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories