Wata Mata Ta Suma Sau Biyu A Ƙoƙarin ta Na Ɗanɗana Yadda Musulmai Ke Ji A Azumi

Wata Mata mai suna Eniola Fagbemi Ta yi matuƙar jinjina wa musulmai yadda  suke jure azumi,sakamakon yinƙurin gwada wa da tayi wanda hakan ya Kaita ga suma sau biyu.

Matar wacce ta shaida cewar ita Kirista ce, amma sai dai shi mijinta Musulmi ne, ta bayyana cewar tana matuƙar sha’awar yadda Musulmi ke yin azumi.

” Kullum sai na tashi ƙarfe 4:30am domin dafawa mijina abincin sahur, Wanda hakan ne yasa naje cewar inaso In gwada yin azumin nan.”

Ranar da ta ɗaura niyya bayan ta yi sahur,ƙarfe 10 na safe cikin ta ya fara kiran ciroma amma ta yi hakuri ta daure har zuwa ƙarfe 12,inda tace daga nan ne ta fara daina ganewa idanun ta suka fara juyawa.

”Nan take na ɗauki wayata na kira mijina don in sanar masa halin da nake ciki, ya ce min in Yi hakuri indaure, ai ko kafin karfe huɗu na suma sau biyu, sai ganin kai na nayi a asibitin SAANU da ke garin Makola a Ibadan, jihar Oyo.

Eniola ta ce tabbass azumin da musulmai ke yi abun a jinjina musu ne.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories