Mun Kama Ƴan Dabar Da Su Ka Addabi Unguwar Ɗorayi – Ƴan Sanda A Kano

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta tabbatar da kama mutum 22 da ake zargi riƙaƙƙun ƴan daba ne a unguwar Ɗorayi da ke jihar.

Matakin ya zo ne sakamakon ɓarkewar faɗa tsakanin ƴan daba a unguwar ranar Laraba.Wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta ya nuna yadda aka ji wa wasu matasa raunuka a arangamar da aka yi.

Cikin wani bidiyo da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook, ƴan sanda sun bayyana sunan wasu mutum 30 da ake zargi ƴan daba ne da suka addabi Ɗorayi da ke ƙaramar hukumar Gwale.

A cewar kakakin rundunar, kwamishinan ƴan sanda na jihar Muhammad Usaini Gumel zai buɗe sabon ofishin yaƙi da ayyukan daba a unguwar ta Ɗorayi.

Rundunar ta ƙaddamar da shirin tuba da gyara halin wasu ‘yan daba a Kano, har ma ta ɗauki wasu kusan 50 aiki bayan sun tuba.

Kazalika, rundunar ta sha shirya wasanni tsakanin tubabbun ‘yan dabar da kuma ma’aikatanta a matsayin wani sabon salon yaƙi da halayayyar ta daba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories