NDLEA Ta Kama Mutane 279 Tare Da Ƙwato Haramtattun Ƙwayoyi A Kaduna

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun yi nasarar kama mutane 279 da ake zargi tare kuma kwato haramtattun ƙwayoyi masu nauyin kilogiram 2,092.5 a rubu’in farko na shekarar 2024.

 Kwamandan hukumar ta NDLEA reshen jihar Kaduna, Mista Samaila Danmalam shi ne ya sanar da hakan ga Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN a ranar Asabar .

 “A wani samamen da aka kai, hukumar ta yi nasarar kama mutane 279 da ake zargi,  masu safarar miyagun kwayoyi ne,da diloli da kuma masu amfani da su yayin da jami’ai suka tarwatsa gidajen saida haramtattun kwayoyi 39 a wurare daban-daban na jihar.

Yace ƙwayoyin da aka kama sun haɗa da hodar iblis, heroin, wiwi, Tramadol, Methamphetamine da sauran kayan maye masu nauyin kilo 2,092.5.

 Ya kuma bayyana cewa, rundunar ta samu nasarar kama mutane 48, tare da gurfanar da mutane 68 , sannan ta gurfanar da wasu 34 a cikin rubu’in farko na shekarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories