A Ƙarshe Dai Shugaba Tinubu Ya Rattaɓa Hannu Kan Shirin Bashin Ɗalibai

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rattaɓa hannu ya kuma godewa ƴan majalisar dokokin ƙasar game da yadda suka yi dubi kan shirin bashin ɗalibai cikin gaggawa.

 Da yake jawabi bayan sanya hannu kan ƙudirin dokar a fadar sa, shugaban ƙasan ya ce gwamnatinsa ta ƙuduri aniyar tabbatar da ganin cewa an baiwa ilimi kulawa tare da bunƙasa sana’o’i.

Shugaba Tinubu ya ce “A yau na sanya hannu kan takardar shirin bashin dalibai yadda ya kamata. Da farko, ina miƙa Godiya ta ga ƴan Majalisar Dokoki bisa gaggawar da suka yi wajen ganin shirin ya tabbata domin kuwa ilimi shi ne duk wani makamin yaki da talauci.

 “Kuma Mun ƙuduri aniyar tabbatar da cewa an baiwa ilimi kulawar da ta dace tare kuma da bunƙasa sansanonin hannu.

 “Mun kawo wannan shiri ne don tabbatar da cewa babu wani komai talaucin sa da zai gaza samun ingantaccen ilmi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories