Zargin Cin Hanci Da Rashawa Ya Sanya An Dakatar Da Ganduje Daga Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC a mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, ta dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin mai ba da shawara kan harkokin shari’a na mazabar Halliru Gwanzo, a lokacin da ya ke gudanar da taron manema labarai da ya gudana a yau Litinin a birnin Kano.

Gwanzo ya bayyana cewa zargin cin hancin da rashawa da gwamnatin jihar Kano ke yi wa Ganduje ne ya sanya su daukar matakin dakatarwar.

“Mun yanke shawarar dakatar da Dakta Ganduje daga jam’iyyar ne saboda girman zargin da ake yi masa,” in ji Gwanzo.

A ranar Alhamis 4 ga watan Afrilu ne gwamnatin ta Kano ta kafa kwamiti guda biyu domin binciken zarge-zargen rashawa da cin hanci da kuma rikicin siyasa tare da ɓatan jama’a da suka faru a karkashin gwamnatin Ganduje.

Har yanzu Dakta Ganduje bai ce uffan ba kan dakatarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories