An Samu Ƙaruwar Hauhawar Farashin Kayayyaki A Najeriya

Hukumar ƙididdiga a Najeriya ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris.

A shafinta na X, hukumar ta ce hauhawar ta ƙaru ne daga kashi 31.7 cikin 100 na watan Fabarairu.

A cewar hukumar, wannan ya nuna hauhawar farashi ta ƙaru da da kashi 11.16 cikin 100 a watan Maris ɗin 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Maris na 2023 da ya kasance kashi 22.04 cikin 100.

Kazalika ƙididdigar da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashi a Maris ɗin 2024 ta kai kashi 3.02 cikin 100 saɓanin kashi 3.12 cikin 100 da aka gani a watan Fabarairu.

Hakan na nufin a watan Maris, ƙaruwar farashin kayayyaki ba ta kai wadda aka gani ba a watan Fabarairu.

Hauhawar farashi a watan Maris ta faru ne a lokacin da matakan da babban bankin Najeriya ke ɗauka na ɗaga darajar naira kan kuɗaɗen waje suka fara tasiri.

Sauka da tashin farashi kayayyaki da ake samu cikin wata biyu na zuwa ne bayan matakin babban bankin ƙasar ya fito da tsarin sauya fasalin kuɗi, matakin da CBN din ya ce zai taimaka wajen raguwar farashin kayayyaki a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories