Sakamakon JAMB 2024: ‘Yar Jihar Bauchi ta yi bajinta

A ranar Litinin ne, 30 ga watan Mayu, hukumar JAMB mai tsara jarrabawar shiga manyan makarantu ta sanar da sakin sakamakon jarrabawar da dalibai suka rubuta a tsakanin ranar Juma’a, 19 ga watan Mayu, zuwa ranar Litinin, 25 ga watan Mayu.

A sanarwar da hukumar JAMB ta fitar ta bayyana cewa adadin wadanda suka zauna jarrabawar a wannan shekarar ya haura mutum miliyan daya da dubu dari tara (1.9million). An rubuta jarrabawar ne ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa (CBT) a cibiyoyi daban-daban dake fadin kasar nan.

Fabian Benjamin, mai magana da yawun hukumar JAMB, ya bayyana cewa daliban da suka zauna jarrabawar zasu iya duba sakamakonsu ta hanyar aika sakon ko ta kwana mai dauke da ‘UTMERESULT’ zuwa ga 55019 ko 66019 ta layin da suka yi amfani da shi yayin rijistar jarrabawar.

Sanarwar ta bayyana cewa fiye da kaso 70 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarrabawar sun gaza samun makin da ya haura 200. Sannan, kaso 0.5 ne cikin 100 suka samu maki 300 zuwa sama wanda hakan ke nuni da cewa sakamakon na wannan shekara bai yi wani tagomashi ba.

Sai dai, duk da hakan wata ‘yar asalin jihar Bauchi mai suna Kawthar Shehu Toro ta bayar da mamaki bayan ta samu maki 348 daga cikin maki 400 da mutum zai iya samu idan ya rubuta jarrabawar.

A wani sako da tsohon kwamishinan ilimi a Jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde, ya wallafa a shafinsa dake dandalin sada zumunta na ‘X’ wacce aka fi sani da ‘Tuwita’, ya nuna sakamakon da Kawthar ta samu tare da yin tambayar ko ita ce tafi kowa samun sakamako mai kyau a jarrabawar JAMB da aka yi a wannan shekarar.

Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa mahaifin Kawthar, wanda malami ne a jami’ar ATBU dake Bauchi kuma dan uwa gare shi, shine wanda ya tura masa sakamakon jarrabawar ta sakon ko ta kwana (sms). https://twitter.com/Dr_AliyuTilde/status/1786028038796296346

Hukumar JAMB, ta bakin Benjamin, ta bayyana cewa har yanzu bata dora sakamakon jarrabawar na wannan shekarar a shafinta na yanar gizo ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories