Zamu zakulo tare da kakkabe ma’aikata da aka dauka aiki da takardun bogi – FG

Ministan ilimi, Tahir Mamman, yaci alwashin cewa gwamnatin tarayya zata zakulo tare da kakkabe dukkan wasu ma’aikata da aka dauka aiki da takardun karatu na bogi a duk inda suke.

Ministan ilimi, Tahir Mamman, yaci alwashin cewa gwamnatin tarayya zata zakulo tare da kakkabe dukkan wasu ma’aikata da aka dauka aiki da takardun karatu na bogi a duk inda suke.

Mamman ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake karbar rahoton wani kwamiti da aka kafa domin bankado almundahanar takardun karatu.

A ranar Juma’a ne kwamitin, wanda aka kafa a karkashin jagorancin Farfesa Jubrila Amin, ya mikawa Ministan sakamakon binciken da ya gudanar tun bayan kafa shi a watan Janairu.

Ministan ya bayyana damuwa da bacin ransa akan yadda cuwa-cuwar sakamakon karatu ta zama ruwan dare a kasar nan kamar yadda kwamitin ya kara bankadowa.

“Ba zai yiwu mu bar wasu tsirarun mutane su cigaba da zubar da kima da darajar bangaren iliminmu ba.

Ministan Ilimi: Tahir Mamman

“Mai yiwuwa akwai wasu daga cikin ma’aikata a gwamnati da sauran bangarori da aka dauka aiki da takardun bogi wanda akwai bukatar a zakulosu tare da daukan mataki a kansu.

“Abin takaici ne kaga mutum na dauke da sakamakon karatu mai daraja ta farko daga makarantar kasar waje amma da a nan gida Najeriya yayi karatu ko sakamako mai daraja ta uku ba zai iya fita da shi ba.

“Ina mai tabbatar muku cewa ma’aikatar ilimi a shirye take domin daukan matakan da zasu tsaftace bangaren ilimi domin dawo da kima da martabar takardun shaidar kammala karatu,” a cewarsa.

A nasa jawabin, Farfesa Amin ya bayyana cewa akwai bukatar daukan matakan gaggawa domin kiyaye kimar bangaren ilimi tare da bayyana cewa sun ga abubuwa masu takaici a ziyarar da suka kai wasu cibiyoyin karatu dake bada takardar shaidar kammala karatun digiri.

Kazalika, yayi kira ga hukumar kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) akan ta kara saka ido akan irin wadannan cibiyoyi da irin makarantun nan da ake karatu daga gida domin a irinsu ne aka fi aikata cuwa-cuwar takardun karatu.

Farfesa Amin ya kara da cewa akwai bukatar ma’aikatar ilimi ta samar da wani tsari da zai bata damar bibiyar aiyuka da al’amuran manyan makarantun dake kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories