Annoba: Cutar sankarau ta hallaka dalibai 20 a arewacin Najeriya

Ana yawan samun barkewar annobar cutar sankarau a lokacin yanayin matsanancin zafi. Cutar tafi saurin hallaka kananan yara da kuma mutane dake rayuwa cikin wurare masu cunkuson jama'a.

Cutar Sanƙarau ta kashe ɗalibai 20 a Arewacin Najeriya a cewar Kwamishinan Ilimi na Jihar Yobe wanda ya bada sanarwar ɓarkewar annobar cutar.

An samu ɓarkewar cutar ne a wasu makarantun Sakandire da ke Jihar ta Yobe. An samu rahoton ɓullar cutar aƙalla sama da ɗari, yayin da mutane uku ke ɓangaren bayar da kulawa ta musamman inda suke karɓar kulawa ta musamman yayin da suke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Cutar Sanƙarau cuta ce mai hatsarin gaske da ke haddasa kumburin wasu sassa na ƙwaƙwalwa da kuma lakar jikin ɗan-adam. Tana iya hallaka mutum idan har ba’a ɗauki matakin gaggawa wajen dakile cutar ba.

Cutar tana iya yaɗuwa kai tsaye ta hanyar mu’amala ko cuɗanya, ko ta hanyar majina, kaki, ko yawu daga wanda ke ɗauke da cutar.

Cibiyar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta wallafa taswirar inda cutar Sanƙarau ta shafa a shafinta na Tuwita.

DUBA WANNAN: Yadda Bincike Ya Gano Muhimmancin Zobo Ga Masu Cutar Hawan Jini

Tabbas canjin yanayi yana kan gaba wajen ta’azzara ƙaruwar yaɗuwar cutar. An samu ɓullar mafi akasarin cutar ne a yankin Arewacin Najeriya.

A cewar Hukumar Lafiya Ta Duniya, an samu rahoton mutuwar mutane 124 a Ƙasashen Afirka ta yamma daga watan Oktoba na shekarar 2022 zuwa 16 ga watan Afrilu na shekarar 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories