Tinubu: Fiye Da Mako Ba A San Inda Ya Yi Aure Ya Tare ba ,Ina Ya Maƙale?

Ɗarururuwan Ƴan Najeriya na cigaba da jefa tambayoyi a kafafen soshiyal Mediya domin neman jin ba’asin ina shugaba Tinubu ya makale,Saboda kimanin makonni biyu kenan tun ranar 28 ga watan Afrilu da aka hange shi a wajen taron tattalin arzikiki na duniya wanda ya gudana a Saudiyya babu wanda ya sake jin ina ya fito, ina zai je .

Abin fargabar shine har yanzu babu wata wasika da ta fito daga fadar shugaban kasar na dalilin da ya sa har yanzu shugaban bai dawo gida Najeriya ba. 

To wannan lamari dai ya janyo kace -nace daga ɓangarori da dama inda wasu ke ganin cewar mai yiwuwa shugaban ya ratse zuwa Paris ne domin duba lafiyar sa .

Ana tsaka da neman ina Shugaba Tinubu ya Yi Aure Ya Tare sai kuma aka ji shima mataimakin sa Kashin Shettima na neman tsallake wa ya bar ƙasa,inda rahotanni suka bayyana cewa mataimakin ya dage daga Abuja zuwa ƙasar Amurka a rana Lahadi, don wakiltar shugaba Bola Tinubu a taron kasuwanci na Amurka da Afirka na 2024.  

Fitowar tafiyar Kashim sai hankalin jama’ar ƙasa ya sake dugunzuma domin kuwa ba a gama neman ina jagora Ya shiga ba shima mataimakin sa na neman ɓallewa.Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar na ɗaya daga cikin mutanen da suka gagara hadiyar yawu sai da suka tofa inda ya wallafa a shafin sa na X yana mai cewa ”Ta ya za a yi ace shugaba bayanan sannan kuma mataimakin sa shima ya tsallake .”

”Bamu taɓa ganin inda aka yi haka ba ace lokaci guda duka shugabanni biyu a neme su a ƙasar a rasa, musamman a yanzu da al’ummar kasar ke fuskantar ƙalubale iri daban-daban. Tambaya anan shine waye zamu Zaƙulo a matsayin jagora mu?

To ko dai muna zamanin mulkin jirgi mara matuƙi ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories