Shan Jiƙo Ya Yi Ajalin Wasu Mutum Biyu A Jihar Ondo

Wasu Mutane biyu Alex Ojolewa da Samuel Alonge ƴan asalin garin Ipe-Akoko da ke ƙaramar hukumar Akoko ta Kudu maso Gabas na jihar Ondo sun gamu da ajalin su ne bayan sun yi tatul da jiƙon maganin gargajiya yayin gudanar da wani buki mai suna Ibogbe.

 Su dai waɗannan mutane sun gamu da ajalin su ne bayan sun isa cikin ƴan uwan su domin gudanar da bukukuwan gargajiya da ake gudanarwa a wannan yanki wanda aka fi sani da ‘Ibogbe’.

 A cewar shaidun gani da ido, sun ce jim kaɗan bayan sun sha maganin, mutanen biyu Nan take suka fara amai har saida ƙarfin su ya ƙare.

Wani mai suna Tunji, ya bayyana cewa, duk da kokarin da aka na garzaya da su sasibiti mafi kusa, abin ya ci turq, wanda hakan ya yi Ajalin su.

Ko da aka tuntuɓi kakakin rundunar yan sandan jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, wacce ta tabbatar da faruwar lamarin, ta bayyana cewa an fara bincike game da lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories