Abubuwa Biyar Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Harajin Da Gwamnati Ta Ƙaƙaba

A wani gagarumin mataki da babban bankin CBN ya ɗauka game da inganta harkar tsaro  ta yanar gizo a Najeriya Bankin ya bayar da umarni ga dukkan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kuɗi da su dinga cire harji kan kowacce hada-hadar Banki da aka yi.

Ƙa’idojin harajin sune kamar haka:

 1 Adadin abinda za a cire: An saita harajin akan 0.5% kan kowani hada-hada da aka yi, kuma an yi hakan ne don ƙarfafa kayan aikin yanar gizo.

2 Tsarin karɓar harajin: Cibiyoyin kuɗi za su cire harajin kai tsaye daga asusun banki a rubuce a asusun bankin ko wani Kwastoma za a ga an rubuta Cybersecurity Levy’.

3 Tsarin Gudanarwa: Dukkanin bankuna sune zasu dinga cire kuɗin ta yanar gizo zuwa asusun tsaro na intanet na ƙasa wanda ofishin NSA (ONSA) ke gudanarwa a kowane wata zuwa ranar kasuwanci ta biyar na wata mai zuwa.

4 Tsawon Lokacin fara Aiwatarwa: Umarnin zai fara aiki ne cikin makonni biyu daga ranar  Mayu 20, 2024, wanda ya sa ake umurtan bankuna su daidaita tsarin su cikin gaggawa.

5. Hukunce-hukuncen rashin bin ka’ida: Rashin saka haraji na iya haifar da hukunci, gami da cin tarar 2% na canjin shekara na cibiyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories