Sarkin Kano Ya Jajanta wa Shekarau Kan Ɓarnar Da Gobara Ta Yi Masa

A ziyarar Jaje da mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kaiwa  tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau don jajanta masa sakamakon wutar gobara da ta laƙume wani sashe na gidan sa.

Idan ba a manta ba a ranar Lahadin da ta gaba ta ne aka sami rahoton tashin gobara a gidan Shekarau inda aka bayyana cewar gobarar ta yi nasarar laƙume wani sashe na ɓangaren sa.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, mai baiwa Malam Shekarau shawara kan harkokin yada labarai, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta tashi ne da yammacin Lahadi ,duk da dai ba a san Musabbabin faruwar lamarin ba an ce wutar ta faro ne daga madafin gidan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories