Alamomin Da Ke Nuna Kamuwa Da Cutar Hassada

Cutar hassada wata cuta ce da ta Addabi al’umma musamman na wannan ƙarni. Duk mai Ƙyashi,baƙin ciki da ni’imar wani,Son ganin an cutar da wani tabbas yana ɗauke da cutar hassada.

  1. Haka kuma:
  2. Kana fatan ni’imar da Allah ya yi wa ɗan’uwanka ta gushe ya rasa.
  3. Ko kana fatan ta dawo hannun ka, shi ya rasa.
  4. Ko kana farin ciki idan wata musifa ta faɗa masa.
  5. Ko kana bakin ciki da wani alkhairi ya same shi.
  6. Ko idan ana yabon sa a gaban ka kana jin rashin daɗi.
  7. Ko idan ana sukar sa a gaban ka kana jin daɗi.
  8. Ko kana jiran ka ji wani mummunan labari game da shi.
  9. Ko idan ka gan shi ka ji rashin daɗi a ranka.
  10. Ko ka haɗa kai da maƙiyan sa don cutar da shi.
  11. Ko ka ji kana ƙin masoyan sa kana son maƙiyan sa.

Idan kana da waɗannan alamun game da wani, to kai mai hassada ne, mummunar hassada, wacce za ta sa ka yi ɓarin duk aiyukanka masu kyau, kuma ba ka isa ka hana Allah Ya yi abinda Ya ga dama ba.

Daga Abba Buhari Abba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories