Jami’an Tsaro ,Mafarauta Sun Bazama Ceto Ɗaliban Da Aka Sace A Kogi

Gwamnatin jihar Kogi ta tura jami’an tsaro da mafarauta cikin daji domin bin sawun ƴan bindiga da suka kai farmaki tare da sace ɗaliban jami’a a daren ranar Alhamis.

In ba a manta ba Dai Masu garkuwa da mutaaki Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence (CUSTEC) da ke Osara, Okene, inda suka yi awon gaba da ɗalibai Tara.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Kingsley Fanwo, a wata sanarwa da ya sanarwa manema labarai jiya, ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin ganin yadda za a kuɓutar da daliban da aka sace.

 “Daruruwan mafarautan yankin da suka san lungu da saƙo na garin da kuma jami’an tsaro su na ta ƙoƙarin ganin an ceto ɗaliban da aka sace .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories