Don ‘yan Najeriya ne – Shettima yayi karin haske kan sabbin haraji

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, a ranar Asabar, ya jaddada kudirin shugaban kasa, Bola Tinubu, na farfado da samar da kudaden shiga a kasar nan.

Shettima ya bayyana haka ne a wajen wani taron da aka yi na rufe taron kwamitin shugaban kasa na kasafin kudi da sake fasalin haraji a ɗakin taron Otal din Transcorp Hilton dake Abuja.

Mataimakin shugaban ƙasar, wanda Dr Aliyu Modibbo, mai bashi shawara na musamman akan harkokin ayyuka ya wakilta, “ya ce gwamnati tana aiki tuƙuru don ganin ta kawo sabon tsarin da zai bunƙasa haraji don taimakawa Najeriya wajen samun ƙarin kuɗaɗen shiga.

Ya yi alƙawarin cewa sabon tsarin zai kasance nagartacce da zai haɓɓaka kasuwanci. ”Gwamnati tana kokarin bunƙasa tsarin haraji da zai haɓɓaka tattalin arziki domin moriyar kowa a Najeriya”, a cewarsa.

Acewar Mataimakin Shugaban Kasa ” Gwamnati zata canja tsarin harajin harajin ne saboda akwai bukatar yin hakan. Sabon tsarin zai tabbatar da adalci da daidaito don cigaban ƙasa”

Ya ƙara da cewa Gwamnatin tarayya zata yi aiki da Gwamnatin Jihohi don aiwatar da tsarin da kuma dorewarsa. Hakan na nufin gwamnatin tarayya zata bada dukkanin gudummawa da goyon baya domin ganin tsarin ya tafi daidai.

KARANTA: EFCC ta haramtawa ofisoshin jakadanci hada-hada da Dalar Amurka

”Maƙasudin wannan tsarin shi ne shine ɓunƙasa tattalin arzikin ƙasa. Gwamnati na son ganin kowa ya mori wannan tsari daga kan ƴan kasuwa zuwa ƴan-ƙasa”.

“Duk da irin jita-jitar da ake yadawa, ba mu zo don mu wargaza wani bangare na tattalin arziki ba, sai don ganin mun tabbatar da tsarin da zai zama mai inganci domin cin moriyar ƴan-ƙasa.”

“Mun taru a wannan wuri ne domin mun samu cigaba daga ɓangaren gabatarwa zuwa aiwatarwa”

”Halin da ƙasa ke ciki shine ya tilastawa gwamnati yin nazarin ja da baya domin gyara ɗamararta don gudun kada wankin hula ya kai ta zuwa dare”.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ne ya rawaito

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories