Kotu Ta Sakaya Matar Da Ta Saci Sa Hannun Marigayi Abba Kyari

Wata babbar kotu da ke Gwagwalada Abuja ta kama Misis Ramat Mercy Mba da laifin satar yin sa hannun tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Marigayi Abba Kyari.

Misis Mercy ta Saci Sa hannun marigayi Abba Kyari ne inda ta aikawa hukumar ICPC saƙon bada Umurnin su ɗauki wasu mutum uku aiki.

 A zaman da aka yi alƙalin kotun Ibrahim Mohammad ya dage yanke hukunci kan wacce ake tuhuma har zuwa ranar 16 ga watan Mayu.

Haka kuma alƙalin kotun Ya bayar da umarnin a cigaba da tsare matar a gidan gyaran hali da ke Suleja.

Dama dai tun shekarar 2022 Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta gurfanar da Misis Ramat kan tuhume-tuhume biyar da suka shafi zamba, da da hannu na jabu wanda ya saba wa sashe na 13 na dokar cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka na 200 da sashe na 320 (b), 366 na  dokokin Penal Code Cap 89 na Arewacin Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories