Kungiyar kwadago ta fice daga tattaunawa da gwamnati akan karin albashin ma’aikata

Majiyar WikkiTimes ta sanar da ita cewa gwamnati bata zo da alkaluma ko wani karin bayani da zai bayyana dalilinta na kafewa akan yin tayin da ta gabatar yayin ganawarsu da NLC ba.

Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta fice babu shiri daga tattaunawa da gwamnati akan maganar Karin albashin ma’aikata.

Ana tattaunawar ne a tsakanin kingiyar kwadago da gwamnatin da kuma bangaren hadakar kungiyar ma’aikata a masana’antu.

Kungiyar kwadago ta fice daga tattaunawar ne bayan gwamnati ta kafe akan mayar da mafi karancin albashi zuwa N48, 000 a karamin mataki da Kuma N54, 000 a babban mataki.

NLC ta bayyana tayin da gwamnati ta yi a matsayin abin dariya Kuma abin wasa.

\

Majiyar WikkiTimes ta sanar da ita cewa gwamnati bata zo da alkaluma ko wani karin bayani da zai bayyana dalilinta na yin tayin da ta gabatar yayin ganawarsu da NLC ba.

KARANTA: Kuma dai: ASUU ta yi barazanar sake tsunduma yajin aiki

Tun a kwanakin baya ne NLC ta fitar da bayani Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

A yayin ganawar, hadaddiyar kungiyar ma’aikatan masana’antu ta bayyana ce babu mambobinta dake biyan ma’aikaci kasa da N78, 000 ba a wata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories