Matashiya ‘yar shekara 33 ta zama alkaliya a babbar kotun jihar Jigawa

Wata matashiyar Lauya mai neman gurbi a karatun digiri na uku a bangaren shari'a mai suna Nilfa Abdullahi Gambo ta zama alkaliya a babbar kotun Jihar Jigawa.

Wata matashiya, ‘yar shekara 33, mai neman gurbi a karatun digiri na uku (PhD) kuma mahaifiyar ‘ƴa’ƴa huɗu ta zama aƙaliyar babbar Kotun Jihar Jigawa.

Matashiyar mai suna Nilfa Abdullahi Gambo na daga cikin jerin Alkalan Manyan Kotuna da Majalisar kula da bangaren shari’a ta Kasa ta amince da su a matsayin alkalai a makon da ya gabata.

Nilfa mace ce mai hankali, ƙwazo da kirki.

Naɗin nata ya samo asali ne daga irin ƙwazon da ta nuna da kuma zaburarwa da bada ƙwarin gwuiwa ga matan da ke da muradin zama lauyoyi da sauran matakai baki daya.

WikkiTimes Hausa ta ci karo da wadannan bayanai ne daga shafin dandalin sada zumunta na ‘X’ na lauya mai sharhi akan al’amuran yau da kullum, Bulama Bukarti.

”Bayan kammala karatunta na digirin farko a Jami’ar Bayero ta Kano, Nilfa ta shiga makarantar horon lauyoyi inda ta samu shaidar zama lauya a shekarar 2013.

”Daga nan ta samu shaidar kammala karatun digiri na biyu daga jami’ar SOAS da ke birnin Landan, kasar Ingila, inda ta kware a fannin dokokin tattalin arziki na kasa da kasa tare da mai da hankali kan nahiyar Afirka.

”Ita ɗin kuma ƙwararriyar mai shiga tsakani da sasantawa ce ta ƙasa da ƙasa, kuma memba a wasu kungiyoyin kwararru na kasa da kasa da suka hada da CIArb UK da ICMC.

”A baya ta yi aiki a matsayin mataimakiyar bincike, magatakarda, kuma mai shiga tsakani a kotun NICN a karkashin alkalai da dama na wannan Kotun.

”Nilfa ta yi nasarar cimma waɗannan duka tana ‘ƴar shekeru 33, yayin da kuma ta haifi ‘ya’ya hudu da take reno duk da haka,” kamar yadda Bukarti ya wallafa.

KARANTA: Kano: Kotu ta daure ‘yan kasuwar canji 17 na tsawon wata shida

Sannan ya cigaba da cewa, ”Ita fitila ce mai haska gaskiyar cewa ba zaɓi bane tsakanin aiki ko iyali ba. Nilfa tayi nasarar haɗa duka biyun a lokaci guda kuma duk ta yi nasara.

”Bawai ga iya danginta da mahaifinta, Abdullahi Gambo, kaɗai ta zama abar alfahari da tunƙaho ba, Nilfa abar alfahari ce ga ɗaukacin Arewacin Najeriya.

”Babu shakka, mijin Nilfa ya cancanci yabo bisa goyon bayanta wajen ganin ta cimma muradanta tare da bata dukkanin gudummawar da ta dace”.

Bukarti ya kara da cewa, ”Jihar Jigawa ta ƙara zama zakaran gwajin dafi, ta ƙara lashe kambun tafiya da matasan lauyoyi masu jini a jika a fannin shari’a.

”A baya bayan nan, jihar Jigawa ta naɗa matashi, Auwal Ya’u, a matsayin alkali a babbar kotu kuma mun yi murna tare da yabawa Jigawa bisa kokarin gwamnatin jihar wajen tafiya da matasa a dukkan al’amuranta.

”Yanzu ma an sake kwatawa, Jihar Jigawa ta sake samar da Nilfa. Wannan al’ada da hukumar shari’ar Jigawa ta runguma wajen naɗa matasan lauyoyi a matsayin alƙalai zai inganta jihar ta hanyoyi daban daban da kuma dauƙaƙa darajar bangaren shari’a. Ku rubuta ku ajiye”.

A karshe, Bukarti da sauran wasu da suka tofa albarkacin bakinsu sun yi addu’ar Allah ya yi jagora, ya kiyaye, ya kuma kare Mai girma, Mai shari’a, Nilfa. Ya bata damar yin adalci ba tare da nuna tsoro ko son rai ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories