An Yi Bikin Buɗe Sabon Gidan Gwamnatin Jihar Bauchi

Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima a jiya Asabar ya ƙaddamar da buɗe sabon gidan Gwamnatin Jihar Bauchi wanda Gwamna Bala Muhammad ya gina a ƙoƙarin sa na sauƙaƙa aiki da kuma kyautata harkokin mulki.

Da ya ke magana a wajen taron, Shettima ya yabawa irin ƙwazon da Gwamna Bala ya yi wajen ganin ya zamanantar da jihar, ya kuma yi kira ga Gwamnonin Arewa maso gabas da su maida hankali wajen ganin sun aikata kyawawan ayyuka.

Ya na mai cewa, “Gaskiya Gwamnonin Arewa maso gabas suna ƙoƙarin sosai wajen kyautata mulki”, Ya kuma yi kira garesu da su zage damtse wajen ƙoƙarin kyautata rayukan al’ummar su. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories