Kotu ta lissafa sharudan bada belin Abba Kyari biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa

Alkalin kotun, Jastis Emeka Nwite, ya bukaci Abba Kyari ya ajiye miliyan hamsin da Kuma mai zai tsaya masa wanda shi ma zai ajiye miliyan hamsin.

Wata babbar kotu dake zamanta a Abuja ta amince zata bayar da belin babban jami’in dan sanda da aka dakatar daga aiki, DCP Abba Kyari, biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa.

Belin, na wucin gadi, na zuwa ne bayan Abba Kyari ya shafe fiye da shekara biyu a tsare.

Alkalin kotun, Jastis Emeka Nwite, ya bukaci Abba Kyari ya ajiye miliyan hamsin da Kuma mai tsaya masa wanda shi ma zai ajiye miliyan hamsin.

A cewar alkalin, wanda zai tsayawa Abba Kyari dole ya kasance lauyansa Kuma sai ya ajiye takardar shaidarsa ta zama lauya a wurin magatakardar kotun.

Jastis Nwite ya sanar da sharudan Samun belin ne gabanin zaman kotun wanda za a yi ranar 31 ga watan Mayu domin sauraron bukatar neman bayar da belin Abba Kyari.

Lauyoyin Abba Kyari sun rubuta takardar bukatar neman belin wanda suke karewa biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Yachilla Kyari, a ranar 5 ga watan Mayu.

DUBA WANNAN: Matashiya ‘yar shekara 33 ta zama alkaliya a babbar kotun jihar Jigawa

A baya sau biyu kotu tana watsi da bukatar Abba Kyari ta neman beli duk da ya yi korafin cewa ana yunkurin kashe shi a gidan yari na Kuje dake Abuja.

A shekarar 2022 ne aka gurfanar da Abba Kyari a gaban kotu bisa tuhumarsa da hannu a harkallar miyagun kwayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories