In Kin Kasance Cikin Jerin Waɗannan Mata Za Ki Yi Wahalar Samun Miji

Lokuta da dama mata na samun jinkiri wajen samun abokin zama wato mijin aure,sakamakon waɗan su halayya da suke kasancewa katanga tsakanin mace da yin aure,Ya ke ƴar uwa In kin kasance mai ɗaya daga cikin waɗannan halayyar to fara neman yadda zaki nemo wa kanku sauyi domin dacewa da abokin zama:

Mace Mai tsananin kyau 

 Ikon Allah ne kawai ya ke iya zaunar da kyakkyawar mace a ɗakin miji  saboda zata dinga tunanin ai ko  rabu da mijinta wani wanda ya fushi zai zo saboda tana da kyau.

 Yawan Roƙo

 Yawancin kyawawan mata sai aka sun jima basu yi aure ba wanda hakan na ba mutane da dama mamaki,Lokuta da dama kyawawan mata na amfani da Kyau da suke da shi ya zamoe musu karin samun kuɗi

 Mace Mai Ilimi 

Mace mai digiri, masters, PhD itama ikon Allah ne kawai ke zaunar da ita a gidan aure

.kwalin karatun kan sa mace ta ji cewar ta isa ta tsaya da ƙafafun ta.

 Mace Da ta fito gidan ƙudi

Duk Matar da ta taso a gidan masu arziki yana da wahala ta iya zaman aure saboda burin ta kawai kar rayuwa ya sauya.Basa ƙaunar a Nadu shawara.

Mace Mai yawan ibada

Mafi yawan mata masu yawan ibada aure na musu wwahala yawancin su zawarawa ne .Saboda basa iya ba wa kansu lokacin kula da miji,shawara In ba ta malamai ba mijin su bai isa ya basu ba.

Sabida haka yake ƴar uwa ji da kai ba naki bane,biyayya kula da miji sunada matuƙar tasiri a zamantakewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories