Na Karɓi Ƙaddarar Duk Hukuncin Da Aka Yanke-Sarkin Gaya

Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir, Sarkin Gaya da aka sauke ya ce babu ja ya amince  tsigen shi da aka yi hukunci ne na Ubangiji.

 Alhaji Aliyu na daga cikin sarakuna biyar da Gwamna Abba Gida Gida ya soke masarautun su a jihar Kano.

Da yake mayar da martani kan matakin da gwamnan ya dauka a wata hira da BBC Hausa ta yi da shi,tsohon sarkin da aka tsige ya ce shi bai riƙe kowa a rai ba.

 Ya kuma ƙara da cewa ba shi da niyyar ƙalubalantar matakin a kotu .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories