Boko Haram Sun Kashe 8, Sun Yi Garkuwa da Mutane Da Dama A Niger

Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton ƴan ta’addan Boko Haram ne sun kashe akalla mutane takwas tare da yin garkuwa da kimanin mutane 160 a ƙauyen Kuchi da ke ƙaramar hukumar Munya ta jihar Niger.

 A cewar shugaban ƙaramar hukumar ta Munya Aminu Na-jume ya ce Harin ya yi sanadiyyar tarwatsa ɗaruruwan mazauna yankin.

 “Mutane da yawa sun rasa matsugunansu.  A Yanzu haka mun gano sansanonin IDP daban-daban. Ba a taɓa samun hari irin wannan mummunan harin ba,wanda ya kai ƴan Ta’addan shafe sa’o’i takwas suna gudanar da ayyukansu,” Na-jume ya shaida wa BBC Hausa.

Ya bayyana cewa cikin mutane 160 da aka sace har da Sarkin Hausawan yankin wanda bashi da ma lafiya, haɗe da mata da yara da kuma tsofaffi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories