Shugaba Tinubu Zai Kaddamar da Tsohuwar Waƙar Taken Najeriya

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce Shugaba Tinubu ya kai ziyara Majalisar Dokoki a yau Laraba don ƙaddamar da tsohuwar wakar kasa mai taken “Nigeria We Heil Thee.”

 Ya ce majalisu biyu ne su ka amince da dokar mayar da tsohuwar taken Najeriya a ranar Larabar da ta gabata wanda shugaban ƙasa kuma ya sanya wa hannu.

Tinubu ya isa zauren majalisar ne tare da shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, da wasu hadiman gwamnati inda a nan ne aka rera tsohuwar taken da aka yi wa dawo-dawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories