Dagaci ya karbi N700,000 ya bari ‘yan bindiga suka kashe jama’a masu yawa a kauyensa

A makon da ya gabata ne gwamnan jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa ta’addanci ya zama wani kasuwanci da wasu manyan mutane daban-daban ke cin ribar sa.

A wani faifan bidiyo da ya karade dandalin sada zumunta, gwamna Dikko Radda ya bayyana cewa bai fahimci haka sha’anin ‘yan bindiga keda sarkakiya ba sai bayan ya zama gwamna.

Dikko Radda ya bayyana cewa “hatta mutanen da baka taba tunani ba akwai hannunsu a wannan matsala ta ‘yan bindiga da muke fama da ita a jihar nan”.

A wata hira da ya yi da Jaridar Vanguard bayan cikar sa shekara guda a kan mulki, Dikko Radda ya yi waiwaye a kan irin abubuwan da suka gani a kokarin gwamnatinsa na yakar ta’addanci da ‘yan bindiga.

Da yake karin bayani a kan hakan, Dikko Radda ya bayyana yadda wani Dagaci, a wani kauye da bai bayyana sunansa ba, ya karbi cin hanci daga wurin ‘yan bindiga domin ya bari su shiga garinsa su ci karensu babu babbaka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutanen kauyensa 30.

DUBA WANNAN: Sambisa: Sojoji sun hallaka shugaban kungiyar Boko Haram da ya gaji Shekau

Gwamnan ya kara da cewa talauci yana taka rawa sosai wajen kara rura wutar rashin tsaro a jihar. A cewarsa, abin takaici ne yadda talauci ke saka wasu mutane bawa ‘yan bindiga muhimman bayanai a kan N2,000 kacal.

A karshe, Dikko Radda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na yakar talauci a jihar Katsina domin ganin batagari basu cigaba da amfani da talauci domin cimma miyagun manufofinsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories