Guguwa Ta Yi Ajalin Mutane Huɗu A Kasuwar Baje Koli A Bauchi

Iskar guguwa ta kashe mutane huɗu mutum ɗaya ta jikkata a dandalin Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) da ke cikin garin Bauchi.

 WikkiTimes ta ruwaito cewa dandalin IBB Shi ne ya ɗauki nauyin taron baje kolin hada hadar kasuwanci na Arewa maso gabas da aka yi kwanan nan.

Rahotanni sun bayyana cewa guguwar ta  yi sanadiyyar lalata rumfunan ƴan Gombe da Yobe da ma wasu tantunan ƴan kasuwa da ke cikin wurin.

 Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a yau Lahadi, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakil, ya ce waɗanda abin ya rutsa da su sun hada da Abdullahi Abubakar, mai shekaru 38 da haihuwa daga Bauchi,Ahmed Alfa,Malam Musa da kuma Abdul’aziz Abdulrahman daga jihar Gombe.

Akwai mace ɗaya mai suna Fatima Isa, a halin yanzu tana asibiti yana ƙarɓar kulawa kuma alamun samun sauki na bayyana,” cewar kakakin.

 “Hukumomi sun ɗauki matakan da suka dace, ciki har da ajiye mutanen da suka mutu a dakin ajiyar gawarwaki.kuma ana cigaba da ya yanke irin barnar da ya auku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories