Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Shugaban kasa, Bola Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, da uwargidansa, Remi Tinubu, sun kashe kudin da basu gaza N5.24bn ba a tafiye-tafiye na cikin gida da ketare a cikin wata uku kacal.

Wasu alkaluma da aka bi diddigi ta hanyar amfani da ‘GovSpend’, wani dandalin kimiyya dake bin sahun kudaden da gwamnati ke kashewa, ya nuna cewa shugabannin sun kashe kudin ne a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2024.

Alkaluman ‘GovSpend’ sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta kashe N1.3bn a tafiye-tafiyen shugaban kasa da sauran hidimomi, sannan an kashe N3.53bn wajen musayar kudi da shugaban kasa zai amfani dasu a wasu tafiye-tafiye na ketare guda goma.

Kazalika, gwamnati ta turawa wasu kamfanonin sufuri guda biyu N637.85m don siyawa shugaban kasa tikitin jirgi domin bulaguro a cikin Najeriya da ketare.

Wadannan kudade da aka fitar daga asusun fadar shugaban kasa basu hada da kudaden da aka kashe a kan tawagar da ke raka shugaban kasa ba a duk lokacin da zai fita.

Har ila yau, gwamnati ta sake kashe kudin da yawansu ya kai N12.59bn domin kula da jiragen shugaban kasa a tsakanin wannan lokacin.

A watanninsa shida na farko a kan mulki, shugaba Tinubu ya kashe kudin da yawansu ya kai N3.4bn a irin wadannan tafiye-tafiye, adadin kudin da ya zarce wanda aka ware a kasafin kudin 2023 da kaso 36.

Hakan na nuna cewa gwamnati ta kashe jimillar kudi da suka kai N8.6bn a tafiye-tafiye a tsakanin watan Yuni na shekarar 2023 da watan Maris na shekarar 2024.

Rahoton ya nuna cewa shugaban kasa ya karbi N650m a matsayin kudin ladan aiki daga wadannan tafiye-tafiye.

KARANTA: NLC ta sanar da shiga yajin aikin ‘sai baba ta gani’

‘Yan Najeriya sun dade suna nuna damuwar su a kan yawan tafiye-tafiyen shugabanninsu ba tare da ganin wani sakamako a kasa ba.

A cikin watansu bakwai na farko a kan mulki, Tinubu da Shettima sun ziyarci kasashe 16 tare da shafe jimillar kwanaki 91 a kasashen ketare.

Bincike ya nuna cewa ya zuwa yanzu Tinubu shafe jimillar kwanaki 55 a ziyarar kasar Faransa (sau biyu), Ingila, Guinea Bissau (sau biyu), Kenya, Benin, India, Dubai, Amurka, da Saudi Arabia.

A nasa bangaren, Shettima ya shafe jimillar kwanaki 36 a tafiye-tafiyen da ya yi inda ya wakilci Tinubu a Italy, Russia, South Africa, Cuba, China, da Amurka.

Yayin tattaunawa da jaridar Punch, wani masanin harkokin kudi, Olorunfemi Idris, ya ce irin wadannan bulaguro da shugabanni ke yi zasu iya kara dankon alaka tsakanin Najeriya da sauran kasashen ketare da kawo cigaban tattalin arziki.

KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

Sai dai, ya bayyana cewa kudin da ake kashewa sun yi yawa musamman idan aka yi la’akari da cewa kudaden zasu iya kawo gagarumin gyara idan da za a kashesu a bangaren inganta ilimi ko lafiya.

Cletus Agu, wani farfesan tattalin arziki, ya shaidawa Punch cewa ba laifi bane idan gwamnati ta kashe irin wadannan kudade a tafiye-tafiyen shugabanni matukar ba a saba wata ka’ida ba.

Ya kara da cewa tambayar da ya kamata a yi shine ko kwalliya na biyan kudin sabulu? Ko akwai wata riba ga tattalin arzikin kasa?

Wani masanin tattalin arziki, Dakta Akin Akinlaye, ya ce kamata ya yi shugabannin su rage yawan kashe kudi bisa la’akari da yanayin tattalin arzikin kasa.

Ya bayyana cewa duk da suna da damar yin tafiye-tafiye irin na aiki, amma zai fi kyautuwa su mayar da hankali wajen farfado da tattalin arzikin kasa da ya shiga mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories