Sokoto: Dalilin da ya sa na yanka budurwata a ɗakin Otal- Saurayi

Rundunar Ƴan sanda a Jihar Sokoto tayi nasarar daƙume wani Saurayi mai suna Saifullahi Hassan wanda ake zargi da laifin yanka buduruwarsa har lahira a cikin ɗakin Otal.

A tattaunawarsa da ƴan jarida, Saifullahi ya ce; “Na kawo budurwar tawa ɗakin Otal na ajiye, inda muka ɗan samu rashin jituwa daga nan ne na fusata na sa wuƙa na yi mata yankan rago”

“Amma yanzu na yi dama sosai, sakamakon marigayiyar ta kasance buduruwata na tsawon lokaci, sharrin shaiɗan da ruɗin zuciya ne ya ja mini” a cewar sa.

A wani cigaban kuma tuni, gwamnatin Jihar Sokoto ta garƙame Otal din da Hassan ya tafka wannan ta’asa ta kashe budurwarsa mai ƴ’aƴ’a huɗu.

Yayin rufe Otal ɗin, Kwamishinan kula da harkokin addini na Jihar Sokoto, Dr Jabir Mai hula, ya ce ” Mun garƙame Otal ɗin sakamakon samun korafe-korafen jama’a mazauna yankin kan irin ɓarna da ta’asa gami da yaɗa baɗala da ake a Otal ɗin.

“Mun karɓi tarin korafe-korafe daga mazauna yankin, a wancan satin har kisa aka yi a cikin Otal din, hakan yasa ba tare da ɓata lokaci ba Mai girma Gwamna Ahmed Aliyu ya Umarci a garƙame Otal ɗin don gudun sake afkuwar hakan”

A cewar Kwamishinan Kasuwanci, Dahiru Aliyu, shi ma ya ce “Otal din bashi da shi rijista da gwamnati tare da tabbatar da cewa suna gudanar da Otal din ba bisa ka’ida ba.

KARANTA: Dagaci ya karbi N700,000 ya bari ‘yan bindiga suka kashe jama’a masu yawa a kauyensa

Kwamishinan Ƴan Sanda Jihar Sokoto, Hayatu Kaigama, yayin da suke gabatar da wanda ake zargin ya ce ” a ranar 24 ga watan Mayu, da misalin ƙarfe 6:20 na safe, mun karɓi kiran waya daga wani mutum mai suna Mr John Manajan Otal din Ifeoma dake kan titin tsohuwar tashar jirgin sama wanda ya sanar da mu cewa sun tsinci gawar wata mai suna Balkisu Garba, wadda ake zargin wani baƙo da ba’a shaida ko wanene ba ya kashe ta a ɗakin Otal din su.

”Da jin wannan labari, muka tashi runduna suka fita sumame bisa jagorancin DPO na yankin.”

”Jami’an mu sun samu jaka wadda ya bari a inda ya yi kisan ɗauke da wasu rasitai da layukan waya guda uku wanda da su aka yi amfani wajen gano wanda ake zargin.

”Waɗannan Layukan sun bayyana bayanan wanda ake zargin a matsayin Saifullahi Hassan, namiji, ɗan asalin ƙaramar hukumar Gummi ta Jihar Zamfara, an bi diddigin wanda ake zargin inda daga karshe aka yi nasarar daƙume shi a garin Funtuwa, Jihar Katsina.

”Har yanzu ana ci gaba da bincike inda daga bisani za’a gurfanar da shi gaban kuliya domin ya girbi abinda ya shuka.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories