Ba Ma Cikin Sabgar Yajin Aikin Kungiyar Ƙwadigo-Likitoci A Kano

Ƙungiyar likitocin Najeriya (NMA) reshen jihar Kano, ta ce likitocin ta da ke aiki a faɗin jihar za su ci gaba da aiki duk da yajin aikin da ƙungiyar ƙwadigo ta tsunduma.

Duk da dai sauran jihohi da ke faɗin ƙasar sun tsunduma wanda hakan ya sa aka rufe bankuna, asibitoci, filayen jirgin sama, da kuma ofisoshin gwamnati .

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust a yau Litinin, Sakataren Hukumar NMA a Kano, Dakta Abdurrahman Ali, ya ce “mu ƙungiyar mu babba ce Bama ƙarƙashin NLC saboda haka babu Yajin aikin da za mu tafi.

 “Dukkanin likitoci a jihar za su kasance a bakin aiki a dukkanin asibitoci. Ko da dai zai iya kasancewa ba kowa zai bi dokar ba dan zaka iya zuwa wurin cire fayel ka samu mai cirewan bayanan.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories