Yajin aiki: Gwamnati ta gayyaci NLC tattaunawa a gaggauce

Gwamnatin tarayya ta gayyaci shugabannin kungiyar kwadago (NLC) da takwararta ta TUC domin ganawa a gaggauce dangane da yajin aikin da kungiyoyin suka fara ranar Litinin.

Jaridar TheCable ta rawaito cewa gwamnati ta kira taron gaggawar ne ta hannun hukumar kula da kudin shiga da albashi. Za a yi taron ne ranar Talata.

Taron, wanda zai hada da dukkan bangarorin da ake tattaunawa da su, an shirya shi ne da niyyar kawo karshen yajin aiki tare da cigaba da tattaunawa akan batun karin albashin.

Rahotanni sun bayyana cewa yajin aikin da NLC ta fara ranar Litinin ya samu karbuwa a sassan Najeriya. Ma’aikatan gwamnati basu fita ofis ba, dalibai basu je makaranta ba, bankuna da dama a manyan birane basu bude ba.

KARANTA: Dalla-dalla: NLC ta fayyace dalilin kayyade N615,000 a matsayin mafi karancin albashi

Yajin aiki ya shafi har asibitoci a manyan biranen Najeriya. Jirage basu sauka ko sun tashi ba a filayen tashi da saukar jirage na Abuja da Legas.

Kazalika, kungiyar NLC ta rufe cibiyar samar da wutar lantarki ta kasa, lamarin da ya jefa dukkan kasar cikin duhu.

Hadiman gwamnati da dama da suka hada da ministoci sun fito fili sun nuna rashin gamsuwa da matakin da NLC ta dauka na shiga yajin aiki tare da bayyana hakan a matsayin abinda zai gurgunta tattalin arziki kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories