Tinubu ya kaddamar da bude gidan VP da aka gina akan N21bn

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kaddamar da bude sabon muhallin mataimakin shugaban kasa da aka kashe biliyan N21 wajen gina shi a birnin tarayya, Abuja.

Yayin bikin bude katafaren gidan, wanda aka yi ranar Juma’a, 7 ga watan Yuni, Tinubu ya bayyana cewa an gina gidan ne saboda kima da darajar ofishin mataimakin shugaban kasa ba kawai don Kwalliya ba.

Gidan, Wanda kamfanin Julis Berger ya gina, an fara bayar da kwangilar aikinsa shekaru 14 da suka gabata.

Tinubu, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilta, ya bayyana kudirin gwamnatinsa na yin komai a bayyane tare da yin tsantseni wajen sarrafa dukiyar kasa.

Shettima ya jinjinawa Tinubu bisa jajircewar sa wajen ganin an kammala aikin ginin gidan Wanda gwamnatocin baya suka gaza kammalawa saboda kalubale daban-daban da aikin ya fuskanta.

DUBA WANNAN: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Kazalika, ya jinjinawa gwamnatin birnin tarayya, Abuja, bisa daukar nauyin kammala aikin domin kawo karshen asarar kudaden gwamnati.

An fara bayar da kwangilar aikin ginin gidan a shekarar 2010 akan kudi Naira biliyan N7 amma aka yi watsi da aikin a shekarar 2015, kamar yadda ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories