Ba Za Mu Iya Biyan Mafi Ƙanƙantar Albashin N60,000 Ba – Gwamnoni

Gwamnonin faɗin Najeriya sun fito sun nuna kin amincewar su da biyan mafi ƙarancin albashi na N60,000 wanda gwamnatin tarayya ta gabatar wa Ƙungiyar ƙwadago.

 Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na ƙungiyar gwamnonin (NGF), Hajiya Halimah Salihu Ahmed, ita ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a.

Gwamnonin sun ce biyan albashin N60,000 a gaskiya ba zai yiwu ba saboda ba abu ne da zai dore ba, suka ƙara da cewa idan suka ce za su biya hakan, tabbas wasu jihohi sai sun haɗa da cin bashi kafin su iya biyan albashin ma’aikata.

 Sanarwar ta ƙara da cewa“Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta amince cewa za a sake duba sabon mafi karancin albashi. Haka kuma Kungiyar ta jajantawa ƙungiyoyin ƙwadago a ƙokarinsu na neman ƙarin albashi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories