Kisan Gilla: ‘Yan ta’adda sun fille kan matasa 10 a jihar Neja

Wani gungun ‘yan ta’adda da aka fi zaton cewa mayakan kungiyar Boko Haram ne sun kashe a kalla mutane 20 a wasu hare-hare da suka kai a karamar hukumar Shiroro da Bassa da ke jihar Neja.

Bayan sun kai hari karamar hukumar Shiroro, ‘yan ta’addar sun sake kai wani harin a karamar hukumar Bassa inda suka kashe wasu matasa 10 ta hanyar fille musu kai.

Wasu shaidun gani da ido da suka bukaci a boye sunansu sun shaidawa Rfi Hausa cewa ‘yan ta’addar sun kashe matasan ne saboda sun ki amincewa da tayin su shiga kungiyar Boko Haram.

Wani mazaunin yankin da ya samu damar tserewa yayin harin ya shaidawa Rfi din cewa ‘yan ta’addar sun tilastawa wasu mutanen yankin rike kawunan matasan tare da daukar su hoto.

Shaidun sun bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kai hari garin da tsakar ranar Alhamis tare da daukan lokaci suna cin karensu babu babbaka ba tare da shakkar komai ba.

DUBA WANNAN: Sambisa: Sojoji sun hallaka shugaban kungiyar Boko Haram da ya gaji Shekau

Rfi Hausa ta rawaito cewa majiyarta ta shaida mata cewa ‘yan ta’addar sun ware mutum 20 daga cikin mutanen da suka tattara tare da yi musu kisan gilla.

Wannan sabon harin na zuwa ne wata biyu cif-cif bayan wasu ‘yan ta’addar sun kai hari kauyen Allawa a karamar hukumar Shiroro inda suka fillewa wasu mutane tara kai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories