APC Ta Lashe Dukkan Kujeru A Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Yobe

Sakamakon zabe ya nuna cewa ‘yan takarar jam’iyyar APC ne kadai suka samu nasara a zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar ranar Asabar, 8 ga watan Yuni, a jihar Yobe.

Shugaban hukumar zabe ta jihar Yobe (YOIEC), Dakta Mamman Muhammad, shine ya sanar da sakamakon zaben ranar Lahadi a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

A cewar Dakta Mamman, APC ta lashe zaben dukkan kujerun kananan hukumomi 17 da na kansiloli 178 dake jihar Yobe tare da bada tabbacin cewa an gudanar da zabe na gaskiya kuma cikin zaman lafiya.

DUBA WANNAN: Tinubu ya kaddamar da bude gidan VP da aka gina akan N21bn

“Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben shugabannin kananan hukumomi 17 da kuma kujerun kansiloli 178,” a cewar Dakta Mamman.

Ya kara da cewa YOIEC ta karbi sakamakon dukkan kujerun kansiloli 178 wanda ta tantance, ta tsefe, ta tsaftace kafin ta sanar da sakamako na karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories