Tallafin Mai: An Bankaɗo Badaƙalar Tiriliyan N3.3 A NNPC Zamanin Mulkin Buhari

Wani binciken kwakwaf da wani kamfanin binciken harkokin kudi na kasa da kasa (KPMG) ya gudanar ya bankado yadda aka yi badakala a cikin Tiriliyan N3.3 a kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Binciken ya gano cewar NNPCL ya yi aringizon kudin tallafin man fetur wanda gwamnati ta biya. KPMG ya ce NNPCL ta bukaci Tiriliyan N6 daga wurin gwamnati a matsayin kudin tallafin man fetur.

Sai dai, shugaban NNPCL, Mele Kyari, ya ce har yanzu suna bin gwamnati bashin Tiriliyan N2.8 wanda har yanzu gwamnati ba ta biya ba.

“Tunda muka bukaci Tiriliyan N6 a shekarar 2022 da Tiriliyan N3.7 a 2023, gwamnatin tarayya bata sake bamu wani kudi ba.

“Hakan na nufin kenan gwamnati ta gaza biyan kudin tallafin mai wanda hakan ya sa muka cigaba da daukar nauyin tallafin daga kudaden da suke shigo wa NNPCL.

“Har yanzu muna jirsn gwamnati ta biya NNPC Tiriliyan N2.8 da aka kashe wajen biyan tallafin mai tun kafin gwamnati ta sanar da janye tallafin,” a cewar sa.

KARANTA: Tinubu ya kaddamar da bude gidan VP da aka gina akan N21bn

Kyari ya bayyana hakan ne jim kadan bayan shugaban kasa, Bola Tinubu, ya sanar da cewa gwamnati janye tallafin man fetur.

Sai dai, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar sake gudanar da bincike akan Tiriliyan N2.8 da NNPC ta yi ikirarin cewa tana bin gwamnatin tarayya.

Bayan binciken da KPMG ya gudanar, kudin sun ragu zuwa zuwa Tiriliyan N2.7. Binciken KPMG ya yi duba akan kudaden tallafin man fetur da NNPC ta nema daga shekarar 2015 zuwa 2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories