Jerin Sarakunan Da Aka Hamɓarar Da Su Akan Ƙaragar Mulki Daga 1963 Zuwa Yanzu

Tun bayan kawo ƙarshen Kalifanci Sarakuna da ga yankunan Arewacin Najeriya da dama an hamɓarar da su sakamakon  dalilai mabanbanta.

 Tun zuwan Turawan Mulkin Mallaka, sarakunan gargajiya a Nijeriya suka rasa darajar su da kimar su.

 Haka ma Bayan samun ƴancin kan Najeriya ƴan siyasa da suka gaji turawan mulkin mallaka suma suka ci gaba da nuna ikon su da isa akan sarakunan gargajiya.

 Sakamakon rikicin da ya Kunno Kai a masarautar Kano, WikkiTimes ta yi waiwaye game da manyan sarakunan Arewa da aka tsige daga sarauta tun daga shekarara 1960 bisa wasu dalilai da suka haɗa da tsoma baki a siyasa, rigingimu da gwamnati, da kuma rikicin cikin gida a masarautun.

Ga Jerin Sarakunan Kamar Haka:

Na farko Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi I. Wanda Firimiyan yankin Arewa, Sir Ahmadu Bello ya tsige shi a ranar 10 ga watan Afrilu, 1963. Muhammadu Sunusi Ya kasance ɗaya daga cikin manyan sarakunan wancan zamanin kuma aminin Firayim Minista ne a wancan lokaci.  Rahotanni sun ce dalilan da suka sa aka tsige shi sun hada da rashin jituwar siyasa da Sardauna (Ahmadu Bello), da kuma zargin karkatar da kuɗi.

 Na biyu Alhaji Umaru Abba Tukur.  Sarkin Muri dake Jalingo jihar Taraba.  Kanar Yohana Madaki (rtd) wanda tsohon gwamnan jihar Gongola ne a lokacin shi ne ya tuɓe shi a ranar 19 ga watan Agustan 1986. An ce Madaki ya samu goyon bayan shugaban mulkin soja na lokacin wato Ibrahim Badamasi Babangida.

Na uku shi ne Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris.  A shekarar 1992, Mohammed Dabo Lere, gwamnan jihar Kaduna na wancan lokacin ya dakatar da sarkin Shehu kafin daga bisani ya mayar da kan kujerar sa daga baya. Daga nan Sarki Idris ya cigaba da mulkin Masarautar Zazzau na tsawon shekaru 45.

 Na hudu shine Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki. Kasancewar sa shugaban sarakunan arewacin Najeriya kuma jagoran addinin muslunci a Najeriya ta majalisar koli akan harkokin addinin musulunci . A wancan lokaci Marigayi Janar Sani Abacha Shi ne ya hamɓarar da Dasuki a ranar 20 ga watan Afrilu, 1996, Duk da cewa har zuwa yau babu wani ƙwaƙwaran dalili a hukumance  da ya sa aka dauke shi amma an yi imanin cewa yana da nasaba da harkar siyasa.

 Na biyar shine Sarkin Gwandu, Alhaji Mustapha Haruna Jokolo. Sarkin Ya yi mulki ne a masarautar Gwandu ta jihar Kebbi kafin daga bisani Gwamna Adamu Aliero ya tsige shi a ranar 3 ga watan Yunin 2005. Tun daga lokacin da aka tsige shi aka yi ta tafka rikicin siyasa da gwamnatin jihar Kebbi a wancan lokacin.

Sai kuma Na shida Sarki Sanusi Lamido Sanusi.Sarki Sunusi ya gaji sunan kakansa Muhammad Sanusi shiyasa ake masa laƙabi da Muhammadu Sanusi II. Bayan ya rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Najeriya, ya gaji kakanninsa a matsayin Sarkin Kano na 14 a zuriyar Fulani.  Tsohon Gwamnan Kano Abudllahi Umar Ganduje shi ne ya tsige shi daga kujerar sarauta a ranar 9 ga watan Maris, 2020. Rahotanni sun bayyana cewa gwamna Ganduje ya tsige shi ne sakamakon rashin yiwa gwamnati biyayya sai dai mutane suna hasashen cewar tsoma baki da kushe gwamnati da yake yi da kuma sharhin da yake yi na zamantakewa da sukar wasu manufofi da ayyukan gwamnati.

 Na bakwai shine Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.  A watan Maris din 2020 ne Gwamna Ganduje ya cire shi a matsayin Sarkin Bichi sannan ya daukaka kujerar shi zuwa Sarkin Kano.Sai dai kuma a ranar 23 ga Mayu, 2024 Gwamna Abba Gida -Gida Bayan ya rattaba hannu kan doka ta Masarautar Kano ta 2024 wadda ta soke dokar da aka yi a shekarar 2019 inda hakan ne ya sa aka sake dawo da Sarki Sunsui shikuma Aminu Ado Bayero aka tsige shi wanda hakan ya janyo cece-kuce a tsakanin masarautar ta Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories