Ranar Dimokradiyya: Muhimman Sakonni 8 Daga Jawabin Tinubu

Da safiyar ranar Laraba ne shugaban kasa, Bola Tinubu, ya gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya a bikin ranar Dimokradiyya da ake yi ranar 12 ga watan Yuni na kowacce shekara.

Ga wasu muhimman sakonni guda takwas daga cikin jawabin da Tinubu ya gabatar.

  1. 1. Ya yi jinjina ga tsofin gwarazan ‘yan siyasa da suka sadaukar da rayuwarsu saboda dimokradiyya irinsu MKO Abiola da matarsa Kudirat, Shehu Musa Yar’adua, Alfred Rewane da sauransu.
  2. 2. Ya yabi hazikan ‘yan siyasa da suke raye irinsu Janaral Alani Akinrinade, Farfesa Bolaji Akinyemi, Farfesa Wole Soyinka, Cif Ralph Obioha, Cif Cornelius Adebayo, Uba Sani (gwamnan jihar Kaduna), Sanata Shehu Sani da sauransu, saboda sadaukarwarsu da juriya.
  3. 3. Muhimmancin ‘yan gwagwarmaya da ‘yan jarida: Shugaba Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba zata samu nasarar kawo karshen mulkin soji ba ba tare da gudunmawar ‘yan gwagwarmaya da ‘yan jarida ba.
  4. 4. Dimokradiyya hanya ce ta rayuwa: Tinubu ya bayyana cewa dimokradiyya ba iya zabe ta tsaya ba, hanya ce ta rayuwa cikin ‘yanci, zaman lafiya da lumana.
  5. 5. Kare martabar siyasa: Shugaba Tinubu ya bayyana cewa zai iyakar iyawar sa domin kare kima da martabar dimokradiyya a Najeriya.
  6. 6. Inganta tattalin arziki: Tinubu ya bayyana cewa yana sane da irin mawuyacin halin da ‘yan kasa ke ciki sakamakon sabbin tsare-tsaren gwamnatinsa na gayaran tattalin arzikin Najeriya.
  7. Shugaban ya ce tattalin arzikin Najeriya ya dade da samun tangarda kuma dole gyaransa ya zo da kalubale.
  8. KARANTA: Tinubu ya kaddamar da bude gidan VP da aka gina akan N21bn
  9. 7. Dangantaka da kungiyar kwadago: Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta kama ko muzgunawa kowa ba saboda yajin aikin kungiyar kwadago.
  10. Ya kara da cewa gwamnatinsa ta dimokradiyya ce kuma za ta cigaba da amfani da tattaunawa domin warware dukkan matsaloli.
  11. Kazalika, ya bayyana cewa zai aikawa majalisa kudirin sabon albashin ma’aikata domin mayar da shi doka.
  12. 8. Shuagbanci mai ma’ana: Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba zai taba juyawa ‘yan Najeriya baya ba kuma gwamnatinsa ba zata gaza ba har sai ta inganta rayuwar kowanne dan kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories