Tinubu ya yi tuntuben sahu, ya fadi a wurin taron ranar Dimokradiyya

Wani faifan bidiyo da ya fara bazama a dandalin sada zumunta ya nuna yadda shugaban kasa, Bola Tinubu, ya fadi bayan ya yi tuntuben sahu yayin da yake kokarin hawa bayan motar da zata zagaya da shi a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya isa filin taro na Eagle Square tare da mai dakinsa, Sanata Remi Tinubu, domin shaida yadda bikin murnar ranar dimokradiyya ya ke gudana.

Kafin zuwansa filin taron, shugaba Tinubu ya gabatar da jawabi ga ‘yan Najeriya Ranar Dimokradiyya: Muhimman Sakonni 8 Daga Jawabin Tinubu.

Ya iso filin taron kewaye da dakarun jami’an tsaro da ke gadinsa da kuma hadimansa makusanta.

Tinubu, sanye da farar babbar riga da irin hularsa da kowa ya san shi da ita, ya yi kokarin rike karfe a jikin motar don kar ya kai kasa amma hakan bai kubutar da shi daga faduwa ba bayan ya yi tutuben sahu yayin hawa matakalar da ke bayan motar.

KARANTA: Shettima, Tinubu da matarsa sun kashe N5.2bn a tafiye-tafiye, N12.5bn a kula da jirgi cikin wata uku

Nan da nan jami’an tsaronsa suka garzayo suka kawo masa agaji tare da taimaka masa wajen mikewa ya koma kan digadigansa.

A cikin faifan bidiyon, an ga shugaba Tinubu ya mirje, ya yi fuska, ya tsaya kyam tare da cigaba da dagawa jama’a hannu, alamar da ke nuna cewa karfinsa ya dawo jikinsa kuma yana cikin hayyacinsa.

An cigaba da fareti a filin taron yayin da motar da Tinubu ya hau ta cigaba da tafiya a hankali, shi kuma ya cigaba da dagawa jama’a hannu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories