Bikin Sallah: Sarki Sanusi II Ya Yi Hawan Daba A Kano

Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya gudanar da hawan daba bayan ya sauko daga Sallar idi da ya jagoranta a Masallacin Juma’a na Kofar Mata da ke birnin Kano.

An gudanar da Sallar Idi a masallacin Juma’a na kofar mata saboda mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Asabar ya malale filin sallar Idi.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da sauran hadiman gwamnatinsa sun bi sahun sarki Sanusi, sun halarci Sallar Idi a masallacin kofar mata.

Jami’an soji, ‘yan sanda, Civil defence, da sauransu sun samar da tsaro a masallacin.

Sarki Sanusi ya bi hanyar da Sarki ya saba bi idan zai koma gida bayan sallar Idi tare da tsayawa yana karbar gaisuwa da jinjina daga jama’a da kungiyoyin magoya yayin da yake kan Dokinsa kewaye da dogarai.

Kafafen yada labarai da suka hada da WikkiTimes Hausa sun rawaito cewa Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Kano, Hussaini Gumel, ya sanar da hana hawa yayin bikin babbar Sallah saboda dalilan tsaro.

KARANTA: Kotu Ta Umarci Gwamnatin Kano Ta Biya Aminu Ado Tarar N10m

Sai dai, gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana rashin jin dadinsa bisa umarnin da kwamishinan rundunar ‘yan sanda a jihar ya bayar, yana mai bayyana cewa ba a tuntube shi ba a matsayinsa na lamba daya a sha’anin tsaron jihar Kano.

A daya bangaren, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi sallar Idi a karamar fadar sarki da ke Nasarawa kamar yadda sanarwa ta gabata.

Tun a baya tubabben sarkin ya sanar da soke hawan daba yayin bikin babbar sallah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories