Fitinannen Mai Garkuwa Da Mutane Ya Fada Komar ‘Yan Sanda A Yobe

Jami’an rundunar ‘yan Sanda a Jihar Yobe sun samu nasarar cafke fitinannen mai garkuwa da mutane, Haruna Mohammed, mai shekara 40, dan asalin kauyen Lantewa a karamar hukumar Tarmuwa.

A wani jawabi da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkarim, ya fitar ranar Litinin, ya ce Haruna ya kware wajen neman kudin fansa ko wata kadara mai  daraja daga wurin wadanda ya kama ko danginsu.

DSP Dungus ya Kara da cewa Haruna ya lakanci firgita dangi da ‘yan uwan wadanda ya kama ta hanyar sanar da su ta waya cewa zai illata ko Kuma ya kashe wanda ya kama idan ba a kawo masa kudi ko wata dukiya ba.

Wani mazaunin kauyen Siminti ya sanar da jaridar Leadership cewa Haruna ya nemi ya biya shi miliyan uku ko Kuma ya kashe shi tare da iyalinsa.

DUBA WANNAN: Gawurtaccen dan bindiga, Kachallah Mai Daji, ya shiga hannu

DSP Dungus ya bayyana cewa sun samu nasarar kama Haruna ne da misalin karfe biyu da kwata na ranar Lahadi bayan sun dade suna bibiyar sa da tattara bayanan sirri a kan sa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Yobe, CP Garba Ahmed, ya jaddada cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Yobe zasu cigaba da aiki tukuru domin tabbatar da ganin cewa masu laifi basu samu mafaka a Kauyuka ko biranen jihar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories