Gawurtaccen dan bindiga, Kachallah Mai Daji, ya shiga hannu

Kachallah Mai Daji, Gawurtaccen dan bindigar daji da ya addabi jihohin arewa maso yamma ya shiga hannun dakarun rundunar soji.

Dakarun sojin kasar Nijar ne suka cafke Kachalla a iyakar Najeriya da Nijar yayin da yake yunkurin satar dabbobi.

A cewar wani kwararre a harkar tsaro, Zagazola Makama, Kachalla ya shafe fiye da shekaru goma yana aikata ta’addanci a wasu garuruwan jihar Katsina da Sokoto.

Makama ya Kara da cewa Kachalla ya kashe mutane da dama tare da shafe lokaci yana karbar haraji daga wurin mutanen garuruwan da ya addaba.

DUBA WANNAN: Bashin $350m: Majalisar Jihar Kaduna ta fara binciken El-Rufai

‘Yan bindigar daji sun dade suna cin karensu babu babbaka a jihohin arewa maso yamma musanman a jihohin Katsina, Sokoto, da Zamfara.

‘Yan bindigar kan shiga kauyuka tare da lalata dukiya tare da yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Kazalika, ‘yan bindigar kan kakabawa mutanen garuruwan haraji idan kuma sun ki biya su kai musu hari tare da lalata musu dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories