Yadda Tsananin Zafi Ke Barazana Ga Lafiya Da zama Lafiya

Tsananin zafi da duniya ke fama da shi ya sa kwararru da masana a harkar lafiya nuna damuwar su tare da gargadin jama’a da basu shawarwari a kan hanyoyin kare kai da kiyaye lafiya.

Masanan sun bayyana cewa zafi yana yi wa lafiya illa ta hanyoyi da yawa.

Tsananin zafi kan iya haddasa jin hajijiya, ciwon kai, kyarma da kishin ruwa, wanda zasu iya faruwa ga kowa, matukar mutum bai samu hutawa a cikin rabin sa’a ba.

Babban hatsari ga lafiya da tsananin zafi kan iya haddasawa shine lalata wani bangare na halittun da ke cikin jikin mutum wanda hakan zai iya kaiwa ga an rasa rai.

Sai dai, Masana sun bayyana cewa wani rukunin mutane kamar kananan yara, musamman jarirai, da tsofi da mutanen da ke aiki a cikin rana da kuma marasa matsuguni sun fi kasancewa cikin hatsarin fuskantar illar tsananin zafi fiye da sauran mutane.

Har ila yau, masu dauke da wata rashin lafiya ko yanayi kamar na sarkewar numfashi da ciwon sikari zasu fi saurin samun matsala a lafiyar su sanadiyyar tsananin zafi.

A cewar Masanan, babu wasu alkaluma daga kasashe da dama dake nuna tsananin zafi a matsayin sanadiyyar mutuwar mutane, wanda a sakamakon hakan babu ma’auni da za a iya amfani da shi wajen bayyana illa da barazanar da tsananin zafi yake da ita ga lafiya da dorewar ta.

Amma, rahoton wani bincike da cibiyar Lancet ta fitar a shekarar 2021 ya alakanta mutuwar mutane kusan rabin miliya da tsananin zafi.

Wannan kiyasi bai hada da alkaluma daga kasashen da ke fama da talauci ba, kamar yadda reuters ta wallafa ranar Laraba.

KARANTA: Kashi 28.5% Na Manya ‘Yan 30 Zuwa 70 a Kano Suna Fama Da Hawan Jini

Mazauna kasashen Turai suna cigaba da nuna fargabar ganin maimaita abinda ya faru na mutuwar mutane 61,000 sakamakon matsanancin zafi a kakar zafi ta shekarar 2022, kamar yadda masanna kimiyya suka bayyana.

Masana sun bayyana cewa za a cigaba da fuskantar barazana daga matsalar matsanancin zafi a shekaru masu zuwa sakamakon sauyin da ke haifar da dumamar yanayi.

Domin kaucewa fadawa cikin illolin da matsanancin zafi ke haifar wa, Masana sun bada shawarar a ke yawaita shan ruwa, samun hutu yayin aiki, dakatar da wasu ayyuka a cikin rana, fakewa a inuwa, zama a wurare masu yalwar iska, da duba halin da marasa galihu da kananan yara ke ciki yayin tsananin zafi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories