Za A Sami Ruwa Mai Ƙarfi A Yankunan Kaduna, Taraba, Filato – NiMet

Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen cewar za a yi samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a jihohin Benue, Kaduna, Niger, Plateau da Taraba a cikin kwanaki masu zuwa.

 Haka kuma Hukumar ta kuma ce jihohin Delta, Imo, Cross River, Akwa Ibom, Bayelsa, Ekiti da Osun Suma za su iya fuskantar ruwan sama mai karfi daga yanzu zuwa ranar 24 ga watan Yuni.

 Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin rahoton hasashen yanayi da ta fitar na mako-mako .

Rahoton Ya kara da cewa hasashen zai yi aiki na tsawon kwanaki bakwai wanda zai kare a ranar 24 ga Yuni, 2024.

 Sanarwar ta ce “A cikin mako mai kamawa, ana sa ran Madden-Julian Oscillation (MJO) zai yi karfi a kan yankin yammacin Afirka. Ana sa ran samun kwararar danshi mai kyau da kuma samun ruwan sama kamar da bakin kwarya a sassan Neja, Plateau, Benue, Kaduna, Taraba, Delta, Imo, Cross River, Akwa Ibom, Cross River, Rivers, Bayelsa, Ekiti da Osun.  ”sanarwar ta bayyana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories