Hajjin Bana: Fiye Da Mahajjata 1,400 Ake Zaton Sun Bace Ko Kuma Sun Mutu

Sama da mutum 1,400 ne suka bace ko kuma ake kyautata zaton sun mutu sakamakon tsananin zafi a aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya. An bayar da rahoton mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu daruruwa suka bace.

Zafi ya tsananta yayin da ya yi tashin gwauron zabi sama da 50°C (122°F) a mafi yawan kwanaki, inda ya kai 51.9°C (125.4°F) a Makka a ranar 19 ga Yuni.

Bidiyo masu ban tsoro sun karaɗe shafukan sada zumunta suna nuna- Gawarwakin da aka zubar a gefen hanya. Gawarwakin da ke lullube da likkafani na Musulunci da hukumomin Makka ke aikewa da su.

Jami’ai daga kasashe daban-daban sun ba da rahoton mutuwar mutane a tsakanin ‘yan kasar: –

Masar: akalla mutane 600 sun mutu, tare da rahotannin bacewar mutane 1,400. Wani jami’in diflomasiyyar Masar (wanda ya bukaci a sakaya sunansa) ya tabbatar da lambobin.

Pakistan: akalla mutane 144 sun bata. Ayben Abdel Azim, shugaban kwamitin “nemo wanda suka ɓata ” na Pakistan ya ce “sun gano mutanen da suka bata”.

Iran: Mahajjata 14 ne suka rasa rayukansu, da suka hada da maza 11 da mata uku, yayin da shida suka mutu sakamakon shanyewar ɓarin jiki/bugawar zuciya a cewar Dr. Ali Marashi, shugaban cibiyar kula da aikin hajji da aikin hajji na kungiyar agaji ta Red Crescent.

Iyalan mahajjata da dama suna neman ƴan’uwansu mahajjata da suka ɓace, suna tuntuɓar asibitoci, da kuma miƙa koke ta yanar gizo.

Adadin wadanda suka mutu ya ƙaru saboda riƙon sakainar kashi da mahukuntan Saudiyya suka yi wa lamarin.

Tashar talabijin ta Nabaa, mai yada labarai cikin harshen Larabci, ta zargi mahukuntan Saudiyya da yin rufa-rufa kan adadin wadanda suka mutu.

KARANTA: Hajji: Wata Hajiya daga Najeriya ta kashe kan ta a Madina

Ministan yawon bude ido na Saudiyya, Ahmed bin Aqeel Al-Khatib, ya taya hukumomin kasar murnar “nasarar” da aka samu a aikin Hajjin shekara duk da ƙaruwar mace-mace.

Mahajjata sama da miliyan 2 ne suka halarci aikin Hajji a bana, inda lamarin ya faru a lokacin tsananin zafi a kasar Saudiyya, lamarin da ya kara ta’azzara ƙaruwar mace macen.

Duk da karuwar mace-macen, Ministan yawon bude ido na Saudiyya, Ahmed bin Aqeel Al-Khatib, ya mika sakon taya murna ga mahukuntan kasar kan nasarar da aka samu a aikin Hajjin bana, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito a ranar 20 ga watan Yuni. –

Ahmed ya nuna cewa an samu gagarumar nasara, kuma ya danganta samun nasarar ga umarni, karamci, jajircewa da kulawa ta mai kula da masallatai biyu masu alfarma da kuma bin diddigin kai tsaye da mai martaba Yarima mai jiran gado ke yi, inda ya yi amfani da dukkan karfin da dama wajen hidimtawa baƙin Allah, domin su gudanar da ayyukansu cikin sauki, walwala da kwanciyar hankali,” in ji shi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a cikin jaridar Al Riyadh mallakin gwamnati a ranar 20 ga watan Yuni.
Ahmed bin Aqeel Al-Khatib ya yaba da kokarin mahukuntan Saudiyya ciki har da ma’aikatar lafiya, da kungiyar agaji ta Red Crescent, da jami’an tsaro, saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da nasarar aikin Hajji.

Sai dai kuma hukumomi daga ƙasashe daban daban sun zargi ministan harkokin yawon buɗe ido na Kasar Saudiyya Ahmed ibn Aqeel da yin ƴar burum-burum gami har ma da zuƙi ta malle a rahoton da ya bayar na kammala aikin Hajjin bana lafiya.

Jami’an Iraki, Iran, Jordan, da Siriya sun ba da rahoton mutuwar ‘yan uwansu da dama.

Jami’in diplomasiyyar Masar (wanda ya nemi a sakaye sunansa), Ayben Abdel Azim na ƙasar Iraƙi, Dr. Ali Marashi na ƙasar Iran, da Ahmed bin Aqeel Al-Khatib na ministan harkokin yawon bude ido na ƙasar Saudiyya na daga cikin jami’an da suka yi magana kan dambarwar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

Most Read

Latest stories